Islama
From Wikipedia
Rushe wuraren tarihin muslunci a kasar Saudiyya.
Mujtaba Adam
IRIB Tehran
Idan tarihi da dukkan abinda ya ke kunshe da shi mai dadi da mai daci, “Madubin rayuwa ne” kamar yadda malamansa suka fassarashi, to wuraren tarihi sune kofar fahimtarsa.Kimar wuraren tarihi da matsayinsu bashi da alaka da cewa wadanda suka barsu mutanen kwarai ne ko na banza a bisa mahanga ta kyawawan al’adu. A mahanga ta kur’ani maigirma wuraren tarihi na ashararun mutane wata kofa ce muhimmiya ga “yan baya da za su kallesu domin daukar darasi. "Shin ba su yi tafiya ba ne a doron kasa su ga yadda karshen wadanda suka gabacesu ya kasance? “(Aya ta 10 a cikin suratu Muhammad.).. Ko kuma jan hankalin da Ubangiji ya ke yi wa mazauna tsibirin larabawa akan gurabe da gidajen mutanen Annabi Lut da cewa: “Hakika Lut yana daga cikin manzannin Allah. Yayinda muka tseratar da shi da iyalansa bakidaya. Sai gyatuma wace ta ke cikin wanzuwa (cikin azaba).Sannan muka halakar da ragowar mutanensa. Hakika ku kuna wucewa ta wurinsu lokacin asuba.Kuna wuce su ( gurabai da kufensu) da dare,shin ba za ku yi hankali ba? (wato ku wa’aztu daga abinda kuka gani na kufensu.) (133-138)….Fir’auna Ramsis na biyu ja’irin sarki ne amma duk da haka kur’ani maigirma yake ishara da gawarsa a matsayin wata aya ga “yan baya. “A yau zamu tseratar da gangar jinkinka saboda ka zama aya ga wadanda za su zo a bayanka.”
Rubutattaun bayanai na tarihin “yan baya ba zai kai muhimmancin wuraren tarihi da kayan da suka aikatasu da kansu ba sannan kuma suka barsu a matsayin shaida.Sau da yawa rubutattun littafan tarihi kan dauki salo na siyasa da son rai acikinsu amma wuraren tarihi da kayan da suke kunshe da shi rayayyar shaida ce da take magana kai tsaye da maidubinsu dangane da wanda samar da su. A wurin masana tarihin karkashin kasa (anthropology) mafi muhimmancin abinda dogaro wajen fahimtar yanayin rayuwar magabata sune kayan da suka kera da hannuwansu a lokacin da suke a raye. A kowace rana ta Allah ana sake fahimtar yanayin rayuwar misarawa na dauri ta hanyar abubuwan da suka aikata suka bari alhali kuwa da akawai darurwan littatafai da aka rubuta akansu. A kowace rana ta Allah ana sake fahimtar yanayin rayuwar misarawan dauri ta hanyar abubuwan da suka bari, wadanda darurwan littatafai da aka rubuta akansu basu fada ba.Gine ginen magabata da kayan aikin da suka yi amfani da su a rayuwarsu ta yau da kullum mabudi ne da ya ke warware abubuwa da dama da suka shige duhu dangane da yanayin rayuwar zamantakewa da addini da yanayin tunanin wadanda suka shude.Wannan kadai ya isa ya zama dalili ga al’umma da ta san ciwon kanta ta baiwa kayanta na tarihi daraja da kuma karesu daga salwanta, balle kuma idan wadannan wuraren na tarihi suna da alaka ne da gwarazan mutanen da suka taka rawa wajen gina tarihinta da dukkan wani abu da take takama da shi.
A shekarun baya da basu kai goma ba tsohon ministan mai na kasar Saudiyya Dr.Zaky yameni ya gabatar da jawabi a kwalejin binciken al’adun gabacin duniya da Africa da ke karkashin jami’ar London.jawabin na sa ya kunshi bayani akan aikin da kwararru dari 300 suka yi na hako gidan manzon Allah a birnin makka wanda ya ke a kusa da ka’aba. An kuma nunawa masu halartar wannan jawabi hotunan majigi na gidan da dukkan bangarorinsa. Da dama daga cikin mahalarta wannan jawabi sun zubar da hawaye na shauki saboda ganin hotunan gidan manzon Allah maitsira da aminci da zuriyarsa.Bayan da Dr. Zaky Yamani ya kallama bayani sai ya fadi cewa “Bayan da aka kallama hako gidan an sake rufeshi bakidaya da yashi.Wani daga cikin masu sauraro ya tambayeshi “Menene dalilin da zai sa a rufe gidan da yashi bayan wahalar da aka sha wajen tonoshi? Jawabin da Dr.Zaky Yemani ya baiwa mai tambaya shine. “ A kasar Saudiyya muna da wasu mutane da suke daukar cewa baiwa wuraren tarihi irin wadannan muhimmanci shirka ne.!(qudsul arabi.6/04/2006)
Gidan annabi muhammadu bai yi kama da sauran gidaje ba ta kowace fuska.A cikinsa ne mala’ika Jibra’ilu ke sauka da sakonni daga ubangiji. “Ku ambaci abinda ake karantawa daga ayoyin Allah (Alkur’ani) da hikima a cikin dakunanku.” (Suratul-Ahzab.aya ta 34 ) A cikinsa ne annabi muhammadu ke yin ibada da raya dare da salloli. “Ya wannan mai lullub,ka yi salla dukkan dare sai kadan. Rabinsa ko ka rage wani abu kankane daga cikinsa.Ko ka kara a kansa izuwa sulusinsa.Ka kyauta karatun kur’ani kyautatawa.Hakika da sannu za mu jefa maka Magana mai nauyi(shine kur’ani mai kwarjini don abinda ya ke cikinsa na kallafe kallafe.” (Suratul-mudassir.aya ta 1-5).
Wannan shine dalilin da ya sa Dr.Sami Al-Anqawy wanda ya jagoranci aikin gano wannan gida da hakoshi daga karkashin kasa ya fi kowane masanin ilimin tarihin karkashin kasa murna da farin ciki. Watakila da a ce wanda ya jagoranci aikin hako gidan da annabi Muhamadu ya rayu a cikinsa ba musulmi ba to murnarsa ba za ta gaza ta Dr.Al-Anqawy ba domin kuwa koyarwar da Muhammadu ya zo da ita tana da darajar da ta cancanci a kare duk wani kayan tarihi da suke da alaka da shi balle kuma gidan da ya fara rayuwa a cikinsa.
Da ace wancan gida mai kima ta tarihi da daraja alokacidaya an barshi ne kawai a cikin yashi da sai ace da sauki. Dr.Sami Al-Anqawy wanda kwararre ne a fagen aikin hako wuraren tarihin karkashin kasa a kasar Saudiyya ya kafa cibiya ta musamman(markazu Abhathu hajj) wacce aikinta shine gano wuraren tarihin musulunci da kuma karesu daga salwanta.A ranar 27/3/2006 tashar telbijin din Al-Hurra ta yi hira da shi akan yadda kokarinsa na gwamnatin Ali Sa’ud da malaman wahabiyawa rushe irin wadannan wurare. A cikin bakin ciki da bacin rai Dr. Al-Anqawy ya rika bada labarin kamannin gida na manzon Allah da shine ya jagoranci hako shi.Dakunan cikin wannan gidan guda uku ne babu kari ko ragi.Daki na farko shine wanda manzon Allah ya rayu acikinsa ya ke kuma yin sallaolin dare a cikinsa.Daki na biyu kuwa na matarsa ne Khadijatul-khubra (A.S). Daki na uku kuwa na “yarsa ne Fatimatuz Zahra (A.S.) Adaidai lokacin da Muhammadul-Jasim dan jaridar da ya yi hira da Dr.Al-Anqawy ya ambayeshi makomar wannan gida sai ya sunkuyar da kansa kasa cikin matsanancin bakin ciki yana yin salati ga ma’abocin wancan gida da iyalansa. Wanda duk ya kalli wannan shiri maisuna “Al-majlis” da aka gabatar a ranar litinin 27/03/2006 da karfe 19: 10 gmt zai za ci cewa masu mulki a Saudiyya da malamansu na wahabiya basu da wata nasaba da addinin musulunci ta nesa balle ta kusa.
“Sun rushe gidan sannan sun gina masai a gurbinsa.”!!!!Inji Dr.Al-Anqawy.
“Mutum” Inji Alduos Huxley a cikin littafinsa mai taken After many a summer “Shine garar da ke cinye abinda hannunsa ya gina.” Watakila da a ce wadanda suka rushe gidan annabi muhammadu sannan suka maida shi masai yahudawan sahayoniya ne ko kuma sojojin Amurka da suka shelanta yaki afili akan addinin musulunci to da ba’ayi mamaki ba sosai,amma ace musulmi ne masu takama da bin sunnar annabi ne da riko da ita suka yi wannan danyan aiki da akwai mamaki da ya wuce hankali ya dauka.!.
Da gaske ne cewa rushe wuraren tarihi na addini bai fara daga kan wahabiyawa ba , ba kuma ba zai kare da su ba. Tarihin dauri da yanzu yana cike da labarukan lalata wurare masu tsarki da rusa makabartun abokan gaba.Halifan Abbasiyya Mutawakkil Billahi ya rushe kabarin Imam Hussaini da daidaita shi da kasa a shekarar hijira ta 236,saboda kiyayya da gaba da ke yi da Ahlul Baiti.Irin wannan gabar ce ta siyasa ta sa farkon hawan Abbasiyawa mulki suka rika tono kabarurrukan matattun sararuka Umayyawa suna yi wa kasusuwansu bulala.!A shekarar 1921 da gwamnatin Birtaiya ta raba yankin Ireland gida biyu an rika kona maja’miun yan darikun katolika da kuma protestant.Kowane bangare yana son ganin bayan wuraren addini na abokan hamayyarsa.Kamar yadda fararen fata masu tsattsauran ra’ayi na kungiyar K.K.K. a Amurka suka rika kona maja’miun da bakaken fata ke ibada a cikinsu.Mutanen kasar Sin sun rika kona maja’miun kiristoci a lokacin boren da suka yi wa yan mulkin mallakar Birtaniya 1900. Harin da sojojin India suka kaiwa wurin ibada mafi tsarki na mabiya addinin Sikh Golden Temple a shekarar 1982 saboda su murkushe yan tawaye. Mabiya addinin Hindu sun rushe masallacin Babri da ke Ayodiya na kasar India a 1992.Yan Taliban a kasar Afghanistan kuma suka rushe mutum-mutumin Budha da ke garin Bamiyan. Ayayin yakin Bosnia 1992-1995 Sabiyawa sun kona masallatan musulmi 1,100.Mafi shaharar masallacin da suka kona shine masallacin Atik a ranar 13 ga Maris 1993 wanda aka gina shi a arewa maso gabacin garin Bijeljina tsakanin 1520-1566.
Su kuwa Wahabiyawa suna rushe wuraren tarihin musulunci ne da kabarurrrukan gwarazan musulunci ne da sunan tsarkake addinin musulunci daga shirka da bidi’a.!!!!.Gine gine da suke da alaka kai tsaye da annabi muhammadu da iyalansa da sahabban da duk wani bawan Allah mai daraja a wurin suaran musulmi da kabarurrukansu wanda musulmi ne suka ginasu da hannuwansu,sune wahabiyawa ke rushewa.A cikin shekarar 1816 Sa’ud Ibn Abdul-Aziz Ibn Muhammad Ibn Sa’ud da mayakansa na wahabiyawa sun kutsa cikin birnin Karbala.Ba wanda ya tsira daga takobinsu idan ba wanda ya gudu ko ya buya ba.Tarihi ya yi musu shaida da cewa sun rushe ginin kabarin Imam Hussain (A.S) da balle kofofinsa sannan jagoransu Ibn Sa’ud ya daure dokinsa a jikin kabarin Imam Hussain ya kuma zauna a kusa da shi ya dafa qahwa ya sha.(Kashful-Irtiyab Fi Atba’i Muhammadu Ibn Abdul-wahab.) A cikin shekarar 1924 Abdul-Aziz da mayakan wahabiyawa suka kutsa birnin makka sunnan suka rushe dukkan gine ginen da aka yi makabartar “Mu’alla” wacce ta ke kunshe da kabarurrukan matar annabi Khadijatul-kubrah (As) da kawunsa “Abu-Talib mahaifin Imam (Ali As).A shekarar 1926 sun kutsa cikin birnin madinatul-Munawwara inda suka rushe dukkan gine ginen da musulmin da suka gabaci bullar akidar wahabiyanci suka yi a kan makarbar Baki’a.makabarta ce da ta ke kunshe da kabarurrukan Fatima yan annabi muhammadu da jikokinsa da suka hada Iman Hasan da Zainul Abidin da Imam Ja’afussadiq.(As).Sun rushe dukkan gine ginen da aka yi a makabartar shahidan Uhudu da kabarin Shugaban Shahidai Hamza.A ranar litinin 12/8/2002 motocin buldoza sun nufi ginin kabarin Muhammad Al-Aridhy wanda da ne ga Imam Ja’afarus-sadiq a cikin birnin Madina sannan su ka daidaita shi da kasa bisa umarnin sarakunan saudiyya da kuma sanya albarka daga malaman wahabiyawa…..Hussain Ibn Ali Ibn Hussain Ibn Hassan Ibn Abi Talib ya jagoranci yin bore ga halifa Hadi na daular Abbasiyya ( 169-170 h).Bayan da ya yi shahada tare da mutane 300 an rufesu a wurin da ake kira Fakh wanda shine sunan da ake kiran borensa.Tun wancan lokacin ne ake kiran wannan wuri da sunan makabartar shahidai kuma tana daya daga cikin muhimman wuraren tarihi na makka.Sai dai a cikin shekara ta 2002 gwamnatin saudiyya ta gina hanyar mota wacce ta tsaga makabartar shahidan Fakh gida uku.! Sun kuma sauyawa wannan makabarta suna zuwa makarbartar Abdullahi Ibn Umar alhali littatafan tarihi sun tabbatar da cewa kabarin Abdullahi Ibn Umar yana makabartar Mu’alla ne.!. Buldozar Ali Sa’ud da malamansu wahabiyawa bata tsallake masallacin Masjidul-Ghanam ko masjidul-Bai’a bad a aka gina shi ne adaidai wurin da annabi muhammadu ya karbi bai’ar mutanen makka da suka musulunci bayan Fatahu makka.Sun rusheshi a shekara ta 1325 hijira sannan suka maye gurbinsa da kasuwar saida kayan ruwa da kayan tsaraba a gurbinsa maisuna “Alsuraihy lil Khardhawat wal hadaya.
Wace hujja ko dalili sarakunan Saudiyya da malamansu na wahabiyawa suke da su da za su kare kawukansu agaba ubangiji saboda rushe kabarin mahaifiyar annabi muhammadu Aminatu Bint Wahab a garin Abwa a shekarar1998, da kuma watsawa sauran ginin da ya saura kananzir tare cinna masa wuta kamar yadda Dr. Irfan Ahamd Al-Alawy dan kasar Saudiyya ya fadawa jaridar The Independent ta 19 april 2006.! Watakila da a ce wasu mutane ne masu bakar gaba da annabi muhammadu wadanda kuma ba larabawa ba suka kunna wuta akan kabarin mahaifiyarsa Amina da tarihi ya ambacesu ya kuma la’ancesu. Wulakanta kabari ko da na abokin gaba ne ba al’adar larabawan jahiliyya ba ce balle kuma musulmi.Littafin tarihi na Siratul Halabiyya ya ambato cewa: Bayan yakin Uhudu da kafiran makka suka sha kashi a hannun musulmi Hindu Bint Utbat ta so ta tona kabarin Aminatu Bint Wahab a matsayin daukar fansa.Sai Abu Sufyan wanda a lokacin yana cikin rundudar kafirai ya fada mata cewa: “Kina son ki aikata wani sabon abu da larabawa basu taba aikatawa ba.?”
Wace shirka ma ko bidi’a wahabiyawa suke fada da ita akan gina masallaci a wurin da kabari ya ke? Tabbas ba su jahilci cewa a cikin bakan Hajarul Aswad da ke gab da ka’aba kabarin annabi Isma’ila ne da na mahaifiyarsa Hajara ba.Ba su kuma jahilci cewa masu tsayuwa daga kusurwar arewa maso gabas yayin salloli ba wadannan kabarurruka ne suke shiga tsakaninsu da dakin Allah ba.Ba su kuma jahili cewa sumbartar wannan bakin dutse da ya killace kabarurruka Isma’il da Hajara sunna ce mai karfi ga mai aikin haji ba.!Ba su kuma jahilci cewa Allah ne ya yi umarni ga musulmi cikin aya ta 125 Suratul Baqara da su rika yin salla a daidai Muqamu Ibrahim da ke cikin farfajiyar ka’aba a matsayin wurin yin salla ba.Shi kuwa wannan wuri sawu ne dutse ne da ke dauke da takun sawun kafafun annabi Ibrahim (A.S).
Karnuka bakwai a jere kafin fara bayyanar burbushin akidar wahabiyanci musulmi suna yin gine gine a kabarurrukan iyalan annabi da sahabbai da waliyyai ba tare da sun dauki haka a matsayin ( Bautar kabari ) ba ko bidi’a ba. A wannan tsakanin manyan sahabban ma’aiki da tabi’ai sun rayu ba su kuma hana yin haka ba har sai da Ibn Taimiyya ya bayyana(661-728) da sabuwar akidarsa da ke cewa “Malaman musulunci sun hadu akan cewa baya halarta ayi gini akan kabarurruka” Baya halarta a yi gina masallaci a cikinsu.Baya haharlta a yi salla acikinsu.”!!! Almajirinsa Ibn Qayyim Al-Jauziyya da ya zo bayansa ya maida wannan fatawa a matsayin nazariyya da cewa: “Ya wajaba a rushe gine ginen da aka yi a kabarurruka.Baya halarta a barta matukar da kawai halin rushesu.” Shi kuwa Ibn Abdul-Wahab da ya aka haifa a 1791 ya zama farkon wanda ya kafa tubalin gina gwamnatin da za ta zartar da wannan nazariyya. Shekaru cas’in bayan wafatin manzon Allah wato a lokacin mulkin Walid Ibn Abdul-malik aka shigar da kabarinsa cikin masallacinsa ba tare da tabi’ai da suke a raye ba a wannan a lokacin sun ce yin haka bidi’a ne ko shirka.! Ibn Taimiyya kuma yana raye sarki Sultan Qalawun na daular mamalik ya bada umarnin aka gina qubba a daidai saman kabarin annabi muhammadu a shekara ta 678 hijira.Sarkin daular usumaniyya Sultan Abdul-Hamid kuma ya yi wa wannan qubba fenti mai launin shudin da har yanzu shine a ke sake maimaitawa akowace shekara. Ba wani abu ba ne ya ke hana sarakunan Saudiyya da malamansu na wahabiyawa rushe qubbar da ke saman kabarin manzon Allah ba da ma fitar da kabarin nasa maitsarki daga cikin masallaci sai tsoron fushin al’ummar musulmi. Sun jarraba yin haka alokacin da suka mamaye birnin madina amma boren da musulmi suka yi a cikin wannan birni ya sa Sarki Abdul-Aziz ya ji tsoron faduwar gadon sarautarsa da bai dade da hawa ba ya bada umarnin a tsayar da shi. Shakka babu suna jiran lokaci ne ya yi anan gaba a wani lokaci domin su fitar da kabarin annabi daga cikin masallaci da kuma daidaitashi da kasa kamar yadda suka yi wa kabarin mahaifiyarsa da iyalansa da kuma sahabbansa masu tsarki da aminci.
Abinda ya ke da tayar da hankali shine a daidai lokacin da wahabiyawa suke rushe wuraren tarihin musulunci masu alaka da annabi kai tsaye da iyalansa da kuma sahabansa suna kare duk wani kayan tarihi na sarakunan Ali Sa’ud.! Alkalamin da sarki Abdul-Aziz ya yi rubutu da shi da takobinsa na yaki da tabarau da ya ke sawa lokacin yana raye duk suna nan an adansu a gidan tarihi.Abinda kuma ya fi wannan ban tsoro shine sarakunan Saudiyya da malaman wahabiyawa ba su taba kayan tarihin da suke da alaka da yahudawa ba suna daram kamar yadda suke a lokacin da annabi yake a raye a khaibar.!!!!
A she bai isa a yi tambaya ba cewa wahabiyawa suna son gina wani sabon tsarin rayuwa ne bisa kufai na tarihin musulunci da suka rushe domin kuwa kaso 90 na kayan tarihin musulunci da ke yankin Hijaz sun salwanta a sanadiyyarsu?
|Shafin Farko|